Sunan Allah ya bayyana a jikin bakin bunsuru (hotuna)
Legit.ng ta tattaro cewa an gano rubutun larabci a jikin wani bakin jaririn Akuyan, a wani yanki na Najeriya, kwanan nan.
Koda dai wannan ba shine karo na farko da ake ganin sunan Allah a wurare basu ban al’ajabi ba, amma duk da haka wannan ya jawo hankulan mutane kamar ko wani lokaci.
Kwanan nan Legit.ng ta rahoto cewa wani matashin mutumi ya gano irin wannan rubutu a jikin naman rago guda biyu, wanda aka yanka a lokacin bikin sallar layya na 2017.
Shafin Rariya ta wallafa hotunan bakin bunsurun dauke da sunan Allah fari a jikin sa. Rubutun ya jawo hankulan mutane yayinda suka dauki hotuna da Akuyan.
KU KARANTA KUMA: APC bata shirya ma shugabanci ba – Jigon PDP
Kalli yadda Rariya ta rahoto a kasa:
Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng