Wani Saurayi ya fasa aure saboda Amaryar sa na neman rigar N500,000

Wani Saurayi ya fasa aure saboda Amaryar sa na neman rigar N500,000

- Wani matashi na shirin fasa auren sa saboda kudin rigar amarya

- Ana kokarin a jibgawa wannan saurayi abin da ya fi karfin sa

- Budurwar sa tana nema ya saya mata rigar amare mai tsada

Abu dai na shirin tabarbarewa yayin da wani Saurayi ya ji abin da ya fi karfin sa lokacin da yake shirin aure.

Wani Saurayi ya fasa aure saboda Amaryar sa na neman rigar N500,000
Hoton wata Amarya da rigar ta

Wani saurayi da bai bayyana sunan sa ba kamar yadda mu ka ji daga Jaridar Information Nigeria ya kai kukan cewa Budurwar da yake shirin aura tana neman ya saya mata rigar amare ta N500,000 wanda ta fi karfin samun sa.

KU KARANTA: Dan wasa Cristiano Ronaldo zai yi aure

Wannan matashi dai Likita ne kuma a halin yanzu yana aikin hidimar kasa watau NYSC ya shiga tsaka mai wuya inda ya ga abin na nema ya fi karfin sa. Daktan yace yana tunanin rabuwa da matar don kuwa har an daura auren su a Kotu abin da ya rage shi ne daurin coci.

Shi dai wannan Bawan Allah gaba daya abin da yake shirin kashewa a auren na sa bai wuce N800,000 ba. Sai dai yarinyar tana zama ne a Turai tare da iyayen ta, kuma ya ga tana neman jika masa aiki da sayen wannan riga mai mugun tsada.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Auren jari: Masu auren mata masu kudi sun zama 'yan kasuwa kenan?

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Tags: