Labari cikin hotuna: Gwamna Nasir El-Rufa'i ya yi wa daliban wata makaranta bajinta
Gwamnan jihar Kaduna Mallam nasir El-Rufa'i ya yiwa daliban wata makaranta dake jihar ta Kaduna gagarumar kyauta wadda za ta habaka hanyoyi da inganta karatunsu.
Legit.ng ta ruwaito cewa, gwamnan ya yi tattaki zuwa wannan makaranta ta mata mai sunan Government Girls College Tukur Tukur dake birnin Zazzau a garin Zaria na jihar Kaduna da domin kaddamar da bude raba na'urori da za su habaka da kuma inganta harkar karatun dalibai cikin sauki.
Mallam El-Rufa'i ya rabawa daliban mata na'urori mai kwakwalwa ta hannu na kamfanin samsung galaxy (Samsung galaxy tablet) domin yin karatu cikin sauki da kuma nazari a ilmance.
KARANTA KUMA: Tsagerun Neja Delta sun yi wata muguwar ta'asa a jihar Bayelsa
Jawaban gwamnan sun bayyana cewa, wannan na'urori za su tallafawa daliban wajen daukan darussa ba tare da sun dauki wata takarda ko littafi ba, sannan kuma zai taimaka wajen bunkasar ilimin daliban ta hanyar yin nazari a shafuka daban-daban na yanr gizo.
Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng