Matar tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Sani Abacha tayi shar a sabon hotuna ita da yarta Fatima
Wani gidan daukar hoto, Lilbature sun yada hotunan Mariam Abacha, matar tsohon shugaban kasar Najeriya da yar ta.
An gano Fatima Sani Abacha, tare da mahaifiyarta cikin wasu kyawawan hotuna.
Legit.ng ta tattaro cewa an dauki hotunan ne a wani yanayi na musamman tare da yar tsohon Janar din.
Hotunan sunyi kyau matuka yayinda daga kallon yanayin daukar zaka san uwa da yarn a cikin yanayi mai nishadantarwa da farin ciki. An gano Fatima ta na takun rawar “shoki” a daya daga cikin hotunan.
KU KARANTA KUMA: Lamido ya caccaki Atiku da APC kan zaben 2019
Mai hoton ya wallafa wasu kalamai tare da hoton:
“Soyayyar Ya da Uwa ❤️. Da zaran uwa na bayan mutun toh ya san cewa ya tsira. Ba wai ko wacce uwa ba amma mai girma Hajiya Maryam Sani Abacha. Tsohuwar matar shugaban kasar Najeriya. Mace mai kamar maza!! Inna ki sa mana albarka sannan kiyi mana adduá a karyen wannan taro. Taimako @dee_rhymez"
Kalli karin hotuna a kasa:
Ya kuma wallafa takaitaccen bidiyon ta kalla a kasa:
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng