Sojoji sun kai ma barayin shanu hari a garin Tsafe, sun kashe shugabansu
Bataliya ta 223 dake karkashin rundunar Sojin Najeriya ta daya ta kare wani harin barayin shanu da suka nufi kaiwa a karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.
Kaakakin rundunar Birgediya Sani Usman Kukasheka ne ya bayyana haka a shafinsa na Facebook, inda yace yan bindigan sun nufi garin Tsafe ne da niyyar yin kashe kashe da sace sace a ranar 21 ga watan Satumba.
KU KARANTA:
Sai dai kash! Rundunar Sojan Najeriya ta samu bayanai dangane da manufar yan bindigan, inda nan da nan ta aika da Sojojinta kan hanyar garin Tsafe, nan fa aka yi barin wuta, kar aka kashe dan fashi guda 1.
Da barayin suka fahimci Sojoji sun fi karfinsu, sai sauran suka ranta ana kare, inda yawancin su suka samu ciwuka sakamakon harbin bindiga, tare da zubar da makamansu da baburansu.
Cikin kayayyakin da suka zubar akwai babura guda 7, alburusai guda 6 da bindiga kirar AK 47 guda 2,kamar yadda Legit.ng ta shaida.
Sai dai sanarwar daga bakin Birgediya Kuka-sheka ta bayyana cewa yan bindigan sun hallaka wani jami’in hukumar kare haddura ta kasa kafin zuwan Sojojin.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng