Matar Shugaban kasa ta horar da dubun matasa da mata a Jihar Bauchi
- Uwargidan Shugaban kasa Buhari tayi wa Jama’a abin kwarai
- Matar Shugaba Buhari ta koyawa mata da matasa sana'a a Bauchi
- Ba wannan karo bane farau ba wajen Uwargidan Shugaban kasar
Uwargidan Shugaban kasa Hajiya Aisha Muhammadu Buhari tayi wa mutanen Jihar Bauchi abin alheri yayin da ta horar da mata 1,000.
Mai dakin Shugaban kasa ta horar da matasa ne da mata akalla 1000 a Garin Bauchi ta Kungiyar ta mai suna Future Assured. Uwargidan Shugaban kasar ta koyawa matan aikin hada kayan shafa da na kwalliya da kuma turaren gargajiya da irin su gyale da sauran su.
KU KARANTA: Hadiza Gabon ta kawo ce-ce-ku-ce a zauren zumunta
Haka kuma matasa maza ma ba a bar su a baya ba inda aka koya masu hada turaren mota da kayan rini da irin su maganin kwari wanda za su iya cin abinci da shi. Mai girma gwaman Jihar Bauchi Mohammed Abubakar ya bayyana wannan kwanan nan.
Dazu ku ka ji cewa Gwamnatin Tarayya ta amince a saki wasu makudan Biliyoyin kudi har Naira biliyan 45 ga tsofaffin Ma’aikatan jirgin saman Najeriya.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ministar Buhari tace Atiku ta ke yi a 2019
Asali: Legit.ng