Abubuwa 6 da za su sa ka nemi auren macen Soja
- Idan ka na soyayya da wata macen Soja kayi maza ka aure ta
- Wata Baiwar Allah Sojar ta lissafo amfanin auren mata Sojoji
- Matan Sojin dai na kukan rashin mazan aure sosai a Najeriya
Ashe dai Sojoji mata na da dadin zaman aure amma Jama’a da dama ba su sani ba. Wata Sojar ce dai ta ba ke ba Jama’a shawara su nemi auren Sojoji mata don kuwa su na dadin sha’ani inda ta kawo dalilan ta kamar yadda mu ka samu labari a shafin Yabaleft online.
KU KARANTA: Kamanceceniyar Shekau da Nnamdi Kanu
Daga cikin dalilan akwai:
1. Tana da aikin yi
Tun da tana da sana’a ba ka bukatar ka rika kokarin neman kudin da za ka dauki dawainiyar ta na ko kadan.
2. Cin zarafin ta
Idan har ka auri macen Soja babu wanda ya isa ya ci wa matar ka zarafi don kuwa duk wanda ya gwada ba zai kwana lafiya ba.
3. Za ta kare ka
Bayan za ta kare kan ta to har kai Mijin na ta za ta kare ka idan wata rigima ta taso. Ka ga Mijin Soja ya huta!
4. Rike amana
Idan ka samu Soja babu maganar ta ci amanar ka da wani don kusan babu ma wanda zai yi gangancin kusantar ta don an san babu wasa wajen Soji.
5. Soyayya
Jama’a da dama ba su san cewa Sojojin sun kware a soyayya ba don kuwa sun iya lura da miji da nuna masa kauna.
6. Ilmi
Sojoji na da ilmin bindiga da kuma ilmin dokar kasa don haka ta san abin da ya dace da wanda bai dace ba.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Sojoji sun kaddamar da Rundunar 'Operation Python dance'
Asali: Legit.ng