Yan iska sun kai hari sansanin yan gudun hijira dake Benue, sunyi ma yan sanda da yan gudun hijira duka

Yan iska sun kai hari sansanin yan gudun hijira dake Benue, sunyi ma yan sanda da yan gudun hijira duka

- Wasu yan iska sun kai hari sansanin yan gudun hijira dake jihar Benue

- An zargi yan iskan da satar kayan taimakon yan gudun hijiran

- Sun kuma yi wa jami’an yan sanda da yan gudun hijiran duka

Wasu yan iska sun kai hari sansanin yan gudun hijira dake sansanin Abagana-Agan kan hanyar Makerdi-Lafiya, jihar Benue sannan sun sace bahuhunan shinkafa 200 da sauran kayan agaji.

Yan iskar da suka sauya kamanni a matsayin yan gudun hijira, sun samu shiga sansanin ta tsiya sannan suka far ma yan sandan da aka zuba domin su kare yan gudun hijiran.

Kai tsaye suka wuce dakin da ake ajiye kayan agaji sannan suka fasa kofar da duwatsu da sanduna.

Yan ta’addan dake tsakanin shekaru 14 zuwa 35, sunyi ikirarin cewa suna daga cikin mutanen garin da aka ajiye a sansanin sannan kuma cewa an tauye masu hakki na rashin basu kayayyakin da aka kawo domin wadanda ambaliyar ruwa ya cika dasu.

KU KARANTA KUMA: Shugaban kasa Buhari zai wuce ya ga Likitocin anjima a Landan

Wani dan sanda da ba’a bayyana sunansa ba yayi yunkurin dakatar da mummunan ayyukan matasan amma sun yaga masa khakinsa. Matasan sun kuma yi yunkurin kwace bindigarsa.

Majiyarmu tare da jami’an hukumar bayar da agajin gaggawa sun lura cewa an fasa yawancin dakunan ajiyan kayan taimako.

Wasu daga cikin ma’aikatan da hukumar SEMA ta dauka domin taimakawa wajen rabon kayayyakin taimakon sun bayyana cewa a kullun matasan na kai masu hari a lokacin tashi daga aiki sannan sun kwace jaka mallakar daya daga cikinsu wanda ke dauke da kudi, kayan kwaliya da wayar hannu.

Shugaban hukumar SEMA, Mista Boniface Ortese yayi Allah wadai da harin sannan kuma yace babban sansanin dake kasuwar Makurdi ma ya samu hari sannan kuma ya zamo wajen ayyukan siyasa. Ya kara da cewa ba’a bar tsofaffi ba ma a harin inda ake kwace masu kayayyakin su.

Ortese wanda ya kaddamar da cewa an rufe sansanin guda biyu saboda irin haka, yayi bayanon cewa kwamitin dake kula da wadanda ambaliyar ruwa ya cika dasu karkashin mataimakin Gwamna, Benson Abounu zasu duba gidajen mutane domin duba irin barnar da ruwa yayi sannan su basu kayan taimako.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng