Madalla: Gangar mai ya kara tsada a kasuwar Duniya
- Yanzu haka Danyen mai ya kara daraja a kasuwar Duniya
- Gangar Danyen man fetur ya kai Dala $56 yanzu a kasuwa
- Wannan zai taimakawa tattalin arzikin kasar a shekarar nan
Labarin da mu ke samu yanzu haka shi ne farashin gangar mai ya kara tsada a kasuwar Duniya inda har ganga guda ta kai $56.
Jaridar Daily Trust tace a farkon makon nan ne gangar danyen mai ya kara kudi a kasuwa. An dauki fiye da rabin shekara danyan man bai tashi haka ba. A cikin kwanakin nan ne Gwamnatin Najeriya ta rage farashin fetur a kasar.
KU KARANTA: Wani Sanata ya nemi a binciki mutuwar 'Yaradua
Najeriya dai za ta ji dadin tashin farashin man domin gudanar da kasafin kudin kasar na bana. A kasafin kudin shekarar nan an kiyasta farashin kowane gangar mai a kan kasa $50 wanda a baya aka ji tsoron haka ba zai yiwu ba.
A wata hira da wani Hadimin Shugaba Buhari yayi da Legit.ng Hausa ya bayyana cewa kwalliya ta biya kudin sabulu a Gwamnatin Shugaban kasa Buhari.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ana rikici tsakanin Soji da Biyafara
Asali: Legit.ng