Sahara Reporters tantiran makaryata ne - Fadar Shugaban kasa
- Daya daga cikin masu taimakawa Shugaban kasa ya soki Sahara Reporters
- Bashir Ahmad yace ba yau Jaridar su ka fara gindayawa 'Yan Najeriya karya ba
- Ya yi magana game tattaunawar Mamman Daura da Mahmud Tukur da aka ji
Kwanan nan gidan yada labaran na Sahara Reporters su ka saki wata waya da ake ikirarin na kusa da Shugaba Buhari sun yi a salular tarho har kusan ake kiran iyalin sa da wasu sunaye. Bashir Ahmad yace ba zai yi magana game da iyalan Shugaban ba don bai shafi Gwamnati ba.
Fadar Shugaban kasar tayi magana game da wata tattaunawa da ake zargin an yi tsakanin wani Danuwa kuma na kusa da Shugaba Buhari watau Mamman Daura da kuma Mahmud Tukur a wayar salula. Bashir Ahmad yace a wannan zamani da aka samu cigaba na fasahar zamani komai na iya faruwa.
KU KARANTA: Fadar Shugaban kasa ta maidawa Obasanjo martani
Malam Bashir Ahmad ya ce ba zai ce komai game da sakon da Sahara Reporters din ta fitar ba don babu tabbacin cewa gaskiya ne an yi wannan tattaunawa kuma babu wanda ya isa yace Shugaban kasar yayi murabus kamar yadda aka ji sakon kuma daga bisani an ji Mamman Daura da Mahmud Tukur su na magana game da lafiyar Shugaba kasar.
Bashir Ahmad yace ko a kwanakin baya Jaridar tace Shugaba Buhari zai tafi kasar Amurka bayan Bikin Sallah wanda kuma ya tabbata ba gaskiya bane. Bashir yace da ana tara karyar da Sahara Reporters tayi da an guji labaran su. Ya kare da cewa Shugaba kasar Dattijo ne kuma ba ya fada da 'Yan jarida shi ya sa bai kai Jaridar Kotu ba tuni saboda irin sharrin da su ka saba.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Lauyan Nnamdi Kanu ya kai kuka game da Sojoji
Asali: Legit.ng