Dandalin Kannywood: Kora ta da aka yi a Kannywood 'gaba ta kai ni' - Rahma Sadau

Dandalin Kannywood: Kora ta da aka yi a Kannywood 'gaba ta kai ni' - Rahma Sadau

Shaharariya ‘yar wasan kwaikwayo Rahama Sadau ta bayyana cewa korar da ƙungiyar MOPPAN na masana'antar Kannywood tayi mata ya bude mata kofofin samun nasara tare da karin masoya.

Fittaciyar jarumar ta ayana haka a wata hira ta musamman da tayi da jaridar Guardian lifestyle.

“Ina mai godiya game da haka don ya bude mun kofofin nasara a masana’antar fina-finai. A da Mutane da dama basu san dani ba sai da aka kore ni, ba abun alfahari bane amma ina ganin kaddara ce daga Allah” inji rahama.

Dandalin Kannywood: Kora ta da aka yi a Kannywood 'gaba ta kai ni' - Rahma Sadau
Dandalin Kannywood: Kora ta da aka yi a Kannywood 'gaba ta kai ni' - Rahma Sadau

KU KARANTA: Kwale-kwale ya kife da mutane 150 a Kebbi

Legit.ng ta samu kuma cewa game da dalilin da yasa aka kore ta tauraruwan tace: “Dan kawai na taba mutum aka kore ni. Lamarin addini da Imani tsakanin mutum ne da ubangijin sa. Na taso a matsayin ‘yar arewa , na san iyakoki na kuma na san abubbuwan da ya kamata inyi ko in hana a matsayi na ‘yar arewa kuma musulma”.

Rahama tace hakika ba ko wani matsayi da aka bata tayi take karba indai matsayin ya saɓawa addinin ko al’adar ta.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng