Dandalin Kannywood: Da alama rikicin Rahma Sadau da Nafisa Abdullahi ya zo karshe

Dandalin Kannywood: Da alama rikicin Rahma Sadau da Nafisa Abdullahi ya zo karshe

Da alama dai rikicin da ake ta yayatawa dake tsakanin manya kuma shahararrun jaruman nan mata na masana'antar Kannywood watau Rahma Sadau da Nafisa Abdullahi ya zo karshe komai ya wuce.

Mun dai fahimci hakan ne ta dalilin wani rubutu da jaruma Rahma Sadau tayi a shafin ta na dandalin sada zumunta na Facebook inda take taya abokiyar sana'ar tata watau Nafisa Abdullahi murna dangane da wani muhimmin ci gaba da ta samu.

Dandalin Kannywood: Da alama rikicin Rahma Sadau da Nafisa Abdullahi ya zo karshe
Dandalin Kannywood: Da alama rikicin Rahma Sadau da Nafisa Abdullahi ya zo karshe

KU KARANTA: Fadar shugaban kasa ta caccakin Oby Ezekwesili

Legit.ng dai ta samu cewa Rahma Sadau din ta yada labarin ne da jaridar nan ta Pulse Nigeriya Hausa ta wallafa mai taken 'Nafisa Abdullahi: Jaruma ta zama jkada' inda ta rubuta 'Congrats sis' a harshen turanci da ke nufin 'ina taya ki murna 'yar uwa' da Hausa.

A kwanan baya ne dai cikin watan Afrilu kungiyar mashirya fina finai na Kannywood suka shiga tsakanin jaruman yan fim din nan su biyu Nafisa Abdullahi da Hadiza Gabon bayan wata arkalla data shiga tsakaninsu.

Shaidan dai ya shiga tsakanin jarumai matan ne a jihar Kaduna yayin da suke bakin aiki wajen shirya wani fim a garin na Kaduna, kamar yadda jaridar Rariya ta ruwaito.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng