Fadan sarkin Zazzau tayi kira ga matasa su kyale El-Rufai
- Rahotanni sunce gwamna El-Rufai ne ya bada umurnin hana sarkin zazzau shiga wajen taron bude Olems Hatchery a Kaduna
- Gwamna Nasir El-Rufai ya karyata wannan zargin da akayi masa
- Fadar sarkin Zazzau tayi kira ga matasa su guji daukan wani matakin akan gwamnan
Fadar sarkin zazzau tayi kira ga matasa da kada su dauki wani mataki akan gwamna Nasir El-Rufai duk da zargin sa da akeyi da hannu wajen kunyata mai martaba sarkin zazzau Alhaji Shehu Idris.
Jami'an tsaro dai sun hana mai martaba sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris shiga wajen taron bude katafaren masana'antar sarafa abincin dabobi da kyankyashe kaji na Olam Hatchery and Mill factory da ke Kaduna.
Rahotanni dai sunce gwamna El-Rufai ne ya bada umurnin amma gwamnan ya karyata zargin.
DUBA WANNAN: Babu wanda ya hana ni ganin Buhari a Kaduna – In ji sarkin Zazzau
A ranar Alhamis, matasa da sauran magoya bayan sarkin Shehu Idris zasu hadu a Kofar Doka domin gudanar da zanga-zangan lumana a ranar juma'a.
A wata sanarwa da galadiman zazzau, Alhaji Nuhu Aliyu ya bayar, yayi kira da samarin da su guji aikata duk wani abu da ka iya haifar da fitina ko tashin hankali.
"Kamar yadda koyar wan addinin musulunci ya la'anci duk wani mai tada fitina, fadar Sarkin Zazzau din ta shawarci al'umma da suyi wa shuwagabanni addu'a nasara da zaman lafiya a kasa a maimakon zanga-zanga a jihar Kaduna da kasa baki daya.
Sanarwan ta kara da cewa "Mu dage wajen tabbatar da cewa mun zauna lafiya da juna a maimakon tada hankali''
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kana kana da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng