Surukar Sanata Sani Yerima ta sanya takalman N784k zuwa wajen bikin ta (hotuna)
- An gano surukar wani dan siyasar Najeriya sanye da tsadadun takalma a wajen bikin ta
- An gano amaryar sanye da hadadden takalma wanda farashin sa ya kai sama da naira dubu dari bakwai
- Surukin ta ya kasance tsohon gwamnan jihar Zamafara
Dan tsohon gwamnan jihar Zamfara Sanata Sani Yerima ya angwance da kyakyawar amaryar sa.
Wani mai amfani da shafin Instagram ne yada hotunan kayataccen bikin a shafukan zumunta.
A daya daga cikin hotunan, an gano amaryar da ango suna wani gasa a wajen taron. Sun rike takalmansu a sama.
KU KARANTA KUMA: Jami’an tsaro sun mamaye gidan Nnamdi Kanu - Lauya
An tattaro cewa amaryar ta sanya takalmin Ralph & Russo yayinda take wani wasa wanda aka fi sani da Hikiwale a yaren kasar Japan.
An rahoto cew takalmin ya kai $2,150 kimanin naira 784,750.
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng