Karanta yadda wani Alhajin Najeriya ya tsinto wa kansa rigima a masallacin makka
Mahukuntan tsaro a kasar Saudiyya sun cafke wani Alhaji da kasar Nigeria bisa dalilin daukar wani abinda da fada a kasa shi kuma ya tsinta a harabar Haramin na kasar yayin aikin Hajjin wannan shekarar.
Karamin jakadan Najeriya a kasar ta Saudi Arabia ne dai mai suna Alhaji Sani Yunusa ya bayyanawa majiyar mu inda kuma yace akwai ya kamata Alhazan mu su san cewa akwai kyamarori fiye da dubu biyu a masallacin da kewayen sa, wadanda kenuna dukkan abinda ke faruwa a ciki da harabar masallacin.
KU KARANTA: Manyan yan Najeriya da suka yi fito-na-fito da shugaban kasa
Legit.ng ta samu kuma cewa karamin jakadan na Najeriya ya kuma ce yana shawartar alhazzan da su guji daukar duk wani abu da suka ga ya fadi a haramin da ba nasu bane domin tsira da darajar su da kuma gudun mummunar fahinta daga jami'an tsaro.
Haka kuma karamin jakadar ya zagaya gidajen Alhazan Najeriya domin yi musu wannan gargadin, yana cewa ta haka ne Alhazan na Nigeria zasu tsira da kimar su da martaban su.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a
Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng