Al'ada: Matakan aure a Kasar Malam Bahaushe
Hausa na cikin manyan harsunan Najeriya da ma Afrika musamman ta yamma. Kuma harkar a aure a wajen Malam Bahaushe kan burge wasu al'adun musamman yadda Addinin Musulunci yayi kane-kane a ciki. Haka ya sa auren diyar Bahaushe ya fi araha kan auren wasu Kabilun a Najeriya.
Ka iya cewa matakan aure a Kasar Hausa guda 6 ne:
1. Na gani ina-so
Watau matakin farko kenan da zarar saurayi ya ga tsaleliyar Budurwar da yake so. Daga nan sai ya nemi amincewar iyaye domin jarraba sa'ar sa. A nan ne ake fara binciken addini da nasaba da kuma dabi'ar juna.
2. Soyayya
Daga nan idan an dace sai ka ga an fara kulla alaka har ta kai ga soyayya ana kara kuma fahimtar juna. Idan abu ya gyaru sai ka ji an kai ga tambaya.
KU KARANTA: Boko Haram sun aika wasu lahira
3. Kayan Gaisuwa
Bayan an yi zance iya zance sai dangin namiji su fara kai gaisuwa wajen dangin matar ana mika kayan gaisuwa irin su tufafi da kudi wanda da zarar an karba sai a fara maganar sadaki kuma.
4. Sadaki
A addinin Musulunci yawanci sadakin diya mace ba ya kasa da rubu'i na dinari watau daya cikin hudu na farashin kilo na gwal. Idan akwai wadata kuma iya kudin ka iya shagalinka!
5. Sa rana
Da ance an amince da kudin sadaki sai kuma a sa ranar daura aure. Saurayi zai nemi gidan da za a tare yayin da dangin mace ke kawata gidan.
6. Daurin aure da walima
Shi kenan kuma sai Allah ya kawo ranar daurin aure inda Amarya za ta ci kunshi da duk wata kwalliyar Duniya shi kuma Miji ko wakilin sa a daura masa aure da matar sa. Bayan nan sai ayi addu'o'in da za ayi da kuma 'yar bikin walima domin a ci kuma a sha. A karshe sai a kai amarya gidan mijin ta!
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Bidiyo: Ko ya dace saurayi ya rika zama da budurwar sa kafin ayi aure?
Asali: Legit.ng