Manyan 'Yan APC 4 da su ka nemi Mama Taraba ta sauka daga matsayin ta
- Kwanan nan aka ji wata Ministar Buhari tana yi wa Atiku kamfe
- Jam'iyyar APC mau mulki tayi tir da wannan abun da ya faru
- Wasu sun kira Ministar ta sauka tayi wa Atiku Abubakar aiki
Jama'a da dama sun nemi Ministar Buhari Aisha Jummai Alhassan tayi murabus bayan an ji tayi wa Atiku kamfe na Shugaba kasa a 2019. Daga cikin masu wannan kira akwai:
1. Shugaban APC na Arewa
Mataimakin Shugaban Jam'iyyar na Yankin Arewa maso yamma Inuwa Abdulkadir ya nemi Ministar tayi murabus daga matsayin ta idan har Atiku take shirin yi wa aiki.
2. Gwamna Nasir El-Rufai
Gwamnan Jihar Kaduna El-Rufai yayi kaca-kaca da Ministar yace dama sun gargadi Shugaba Buhari ya guji nada ta cikin Gwamnatin sa domin can ba ta goyon bayan shi.
KU KARANTA: APC ta maidawa Atiku martani
3. Sanata Shehu Sani
Haka shi ma Sanatan na Jihar Kaduna ya nemi Ministar harkokin matar ta sauka daga matsayin ta ta tafi tayi wa Atiku Abubakar aiki.
4. Hon. Danlami Kurfi
Wani Dan Majalisa daga Jihar Shugaban kasar Honarabul Danlami Mohammed Kurfi ya soki Ministar ya kuma kira Shugaba Buhari ya tsige ta don kuwa ba ta yin sa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Gwamnatin Buhari ta rage farashin man fetur
Asali: Legit.ng