Dalilai 3 da za su sanya kara riko da shayi na koren ganye

Dalilai 3 da za su sanya kara riko da shayi na koren ganye

Ga wadansu dalilai guda uku kacal da za su sanya kara riko da shayi na koren ganye

1. Shan shayi yana kara juriya ga ma su motsin jiki. Binciken masana ilimin kumiyya ya bayyana cewa, akwai sunadaran antioxidants a cikin shayi da suke sanya kuzari wajen kone maiko a jikin mutum. Sunadaran antioxidants su na kuma taimakawa wajen bayar da kariyar cutar kansa wato cutar daji, a sassa daban-daban irinsu; mama, hanji, fata, dubura, huhu, hanta, mahaifa, makogwaro da makamantansu.

Dalilai 3 da za su sanya kara riko da shayi na koren ganye
Dalilai 3 da za su sanya kara riko da shayi na koren ganye

2 Koren shayi yana hana kamuwa da bugun zuciya da kuma sauran cututtuka na zuciya. Ana amfani da ganyen koren shayi wajen magance matsalolin cututtukan kwakwalwa irinsu zaucewa da kuma mutuwar barin jiki.

Dalilai 3 da za su sanya kara riko da shayi na koren ganye
Dalilai 3 da za su sanya kara riko da shayi na koren ganye

KU KARANTA: Kashin kadangare ya raba wata budurwa da yatsan ta guda a Jigawa

3. Yana kuma kara inganta kariya ta garkuwar jikin dan Adam, domin akwai kwayoyin halitta daga cikin hasken rana wadanda suke janyo cututtukan fata, irinsu cutar daji ta fata da sauransu.

Dalilai 3 da za su sanya kara riko da shayi na koren ganye
Dalilai 3 da za su sanya kara riko da shayi na koren ganye

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng