Ambaliyar ruwa na barazanar shanye wasu garuruwa a Kogi

Ambaliyar ruwa na barazanar shanye wasu garuruwa a Kogi

- Ambaliyar ruwa na barazanar shanye wasu unguwanni a garn Lokoja

- Hukumar NEMA ta kawo musu dauki

- Mutane na rasa muhallin su sakamakon ambaliyar ruwa

Hukumar NEMA ta kira mutanen da ke unguwar Sarkin Noma da ke karamar hukumar Lokoja da Igala mela da su yi hanzarin barin gidajensu a sakamakon gagarumin ambaliyar ruwan da ya faru a garin.

Ambaliyar ruwa na shirin shanye wasu garuruwa a Kogi
Hukumar NEMA ta kira mutan Kogi su bar yankin da ambaliyar ruwa zai taba

Daga mai magana da yawun hukumar, Malam Sani Datti ya ce 'ma’aikatar tuni ta shirya da Kwamishina na jihar da sauran masu ruwa da tsaki a jihar don samar da tsaro da lafiya ga mutanen da ambaliyar ya afka musu.'

Hukumar ta kara bawa mutane mazauna unguwar da ke wurin da ambaliyar ruwa ya shafa da su hanzarin komawa wuraren da ke sama-sama inda ruwan ba zai shafa ba domin lafiyar su da samar musu tsaro.

DUBA WANNAN: Likitoci sun ki janye yajin aiki duk da alkawarin da gwamnati ta musu

A wancan watan da ya wuce an yi ambaliyar ruwa, sama da mutane 15,000 ne suka rasa mazaunin su sannan kuma a jihar Benue sama da gidaje 2,000 ne suka ruguje a sakamakon ambaliyar ruwa da ya afku.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: