Neja-Delta ta janye wa'adin da ta bawa 'yan Arewa da yarabawan da ke yankin su

Neja-Delta ta janye wa'adin da ta bawa 'yan Arewa da yarabawan da ke yankin su

- Masu fafutukar kafa kasar Naija Dalta sun janye wa'adin da suka dibawa hausawa da yarabawa na barin yankin

- Kungiyar ta kuma janye hare-haren da tace zata kai wuraren matatun man fetur da kuma gurbata hanyoyin da ake sarrafa man fetur din

- Kungiyoyi ne da dama ne suka halarci taron cimma yarjejeniyar a jiya

Kungiyar masu fafutukar kafa kasar Naija Dalta sun janye wa'adin da suka dibawa hausawa da yarabawa na barin yankin na Naija Dalta a wani babban taron da kungiyar hadinkan yan Naija Dalta (PANDEF) ta Shirya a jiya.

Neja-Delta ta janye wa'adin da ta bawa 'yan Arewa da yarabawan da ke yankin ta
Neja-Delta ta janye wa'adin da ta bawa 'yan Arewa da yarabawan da ke yankin ta

Kungiyar, ta bakin shugaban ta, Comrade Imoh Okoko, tace, ta kuma janye hare-haren da tace zata kai wuraren matatun man fetur da kuma gurbata hanyoyin da ake sarrafa man fetur din.

Kuma sun gargadi kungiyoyin yankin a kan duk wani yunkurin kai hari a kan wani bahaushe ko bayarrabe dake yankin hadi da kiran kada wani ko wata kungiya ta ci gaba da fafutukar ganin cewa sun kafa kasar Biafra saboda sun fara tattaunawa da Gwamanatin Tarayya.

DUBA WANNAN: Tompolo ya sha alwashin ramuwar kisan mahaifin sa

Ga wasu daga cikin manyan kungiyoyin da suka yi yarjejeniyar a jiya:

"Niger Delta Watchdogs" ta John Duku, "Coalition of Niger Delta Agitators" ta Janar Ekpo Ekpo, "Niger Delta Volunteers" ta Janar Osarolor Nedam, "Niger Delta Warriors" ta Manjo janar Henry Okon Etete, "Niger Delta Peoples Fighters" ta Manjo janar Asukwo Henshaw, "Bakassi Freedom Fighters" da "Niger Delta Movement for Justice" ta Manjo janar Ibinabo Horsfall.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng