Rake: Ga gardi ga amfanu daban-daban

Rake: Ga gardi ga amfanu daban-daban

Rake wani kara ne mai gabbai kuma cikin sa totuwa sai dai wannan totuwa ta kunshi ruwa wanda ake amfani da shi wajen samar da sukari a kamfaninnika daban-daban.

Rake ya kunshi dimbin sunadarai ma su gina jiki kamar haka; carbohydrates, proteins, calcium, phosphorus, iron, zinc, potassium, vitamins A, B da kuma vitamin C.

Ga wadansu dalilai 9 da za su sanya kara riko da rake

1. Karin karfi a jikin mutum

Sanadiyar yalwar sunadarin glucose a cikin rake, ya sanya shi karawa dukkan mai shan shi karfin jiki.

2. Amfani ga mata masu juna biyu

Rake yana dauke da wani adadi na sunadarin folic acid ko kuma vitamin B9 wanda yake bayar da kariya ga haihuwar jarirai masu nakasashen kashin baya.

Rake: Ga gardi ga amfanu daban-daban
Rake: Ga gardi ga amfanu daban-daban

3. Yana kara karfin hakori da kasusuwan jikin

Akwai sunadaran calcium da phosphorus wanda suke matukar taimakawa wajen kara karfin kashi na jikin dan Adam da hakori, sannan kuma su na taimakawa wajen hana warin baki da rubewar hakori.

4. Taimakawa wajen narkewar abinci

Sunadarin potassium dake cikin rake yana taimakawa wajen rage gubar ciki, wanda wannan guba ita ke hana abinci ya narke da wuri a cikin mutum.

5. Yaki da cutar daji ta mama

Akwai sunadarin flavonoids da yake hana yaduwar kwayoyin cutar daji musamman a maman mata, akwai kuma sundaran potassium, calcium iron, maganesium da suke kara karfafa wannan kariya.

KU KARANTA: Abin Al'ajabi: Sunan Allah ya bayyana a jikin naman ragon layya

6. Waraka daga ciwo mai radadi na makoshi

Akwai yalwar sunadarin vitamin C da yake kawo waraka daga ciwon makoshi mai radadi

7. Taimakawa wajen rage nauyin jiki

Kasancewar rake ba ya dauke da kowane irin maiko, hakan ya sanya shi taimakawa wajen rahe daskararren maiko a jikin mutum, wanda shine jigo wajen kara nauyin jiki.

8. Fa'ida ga masu ciwon sukari

Zakin dake cikin ruwan rake yana da fa'ida ga masu ciwon sukari bisa ga shi kanshi sukarin bayan an sarrafa shi., hakan yana sanya sunadarin insulin ya rinka kewayawa a cikin jikin mutum, wanda daman karanci ko yawan wannan sundari acikin jinin mutum ke sa a kamu da ciwon sukari

9. Yalwar ruwa a cikin jiki

Adaddin ruwan dake cikin rake ya na da girma sosai, hakan ya sanya shi mai taimakawa masu shan shi su zamana cikin yalwar ruwa a jikin su, wanda masana kiwon lafiya suka ce ba ya taba yin yawa a jikin dan Adam.

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Shin wa ya fi shirga karya, maza ko mata?

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng