Kasar Koriya ta kara kirkiro wani babban makamin nukiliya
- Kasar Koriya ta Arewa ta kirkiro wani sabon makamin nukiliya
- Kasar tace ta gama shirya wani babban makami da ka iya aiki a ko yaushe
- Wannan ne karo na 6 da Kasar ta kera makamin nukiliya mai linzami
Dazu muka ji labarin daga BBC cewa Kasar Koriya ta Arewa ta kera wani mugun makamin Nukiliya.
Kasar tace ta gama gwajin sabon makamin na ta wanda shi ne na shida da ta kera. Kasar ta Koriya ta Arewa tace ga dace wajen kirkiro makamin wanda a ko yaushe ana iya harba sa inda aka so.
KU KARANTA: An gayyaci Shugaba Buhari taro wata kasa
Wannan makamin Nukiliyar na Hydrogen ya fi sauran bam karfi. Masana dai sun ce dole sai an bi a hankali don kuwa ba shakka kasar Koriyar ta kai inda ta kai. A dai gwanda wannan makami mai hadari ne a Garin Kilju inda aka saba gwajin makaman kasar.
Kwanaki kun ji cewa Shugaban Kasar Amurka Donald Trump yace idan ta kama sai ya kai wa Koriya ta Arewa hari don ya taka masu burki wajen makami mai linzamin da su ke harbawa.
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Meye abin dubawa wajen fara alaka
Asali: Legit.ng