Yanzu-yanzu: Gwamnati ta rage kudin mai a Najeriya
- Dazu Gwamnati ta rage kudin mai a Najeriya
- Hukumar mai na kasa NNPC tayi wannan sanarwar
- An samu ragin N1 zuwa N2 a farashin man fetur din
Mun samu labari da dumi-dumi cewa Gwamnatin Shugaba Buhari ta rage farashin man fetur a Najeriya.
Hukumar man fetur na kasa watau NNPC ta sanar da cewa an rage farashin fetur da sauran man girki ma gas a fadin Najeriya. Farashin litar dai yayi kasa zuwa N143 ko ka ma N142 daga farashin da Gwamnati ta sa na N145 kwanakin baya.
KU KARANTA: Shugaban Turkiya ya kirae Buhari
Mai magana da bakin Hukumar Ndu Ughamadu ya sanar da wannan dazu a jawabin da ya fitar a yau Lahadi. A kwanakin baya kuma ana saida lita 12.5 na gas kan kudi N4500 wanda yanzu yayi kasa har zuwa N3800 wajen 'yan sari ko N4000 a kasuwa.
Murna zai koma ciki idan aka yi sake a Najeriya don kuwa kwanaki Tsagerun Neja-Delta za su koma fasa bututun mai kamar yadda su ka fada.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Cinikin rago a Najeriya
Asali: Legit.ng