Hawan daushe: Yan kwankwasiyya da Gandujiyya sun sassari juna a Kano

Hawan daushe: Yan kwankwasiyya da Gandujiyya sun sassari juna a Kano

Rahotanni daga jihar Kano na cewa an baiwa hammata iska tsakanin magoya bayan tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso wadanda aka fi sani da yan kungiyar Kwankwasiyya da kuma masoya gwamna mai ci, Abdullahi Umar Ganduje, su kuma yan Gandujiyya

Rahoto daga jaridar BBC na nuna cewa wasu 'yan adawa da ake zargin magoya bayan Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne, sun far ma yan Kwankwasiyyan da sukayi kwalliya da jajayen hulunansu a filin hawa.

Hawan daushe: Yan kwankwasiyya da Gandujiyya sun sassari juna a Kano
Hawan daushe: Yan kwankwasiyya da Gandujiyya sun sassari juna a Kano

Sun kara da cewa yawancin wadanda aka raunata da wuka sun fi yawa da wadanda aka sassara da adda ko tokobi.

KU KARANTA: Hajjin bana: Yan Najeriya 7 sun cika, wasu sun suma a wajen jifan Shaidan

BBC ta bada rahoton cewa wani na hannun daman Kwankwaso ya shaida musu cewa an raunata yan Kwankwasiyya da dama wanda ya hada da tsohon sakataren gwamnatin jihar Kano, Rabi'u Suleiman Bichi.

Hawan daushe: Yan kwankwasiyya da Gandujiyya sun sassari juna a Kano
Hawan daushe: Yan kwankwasiyya da Gandujiyya sun sassari juna a Kano

Zuwa yanzu dai hukumar yan sanda jihar batayi uffin ba game da al’amarin amma kwamishinan yada labarai na jihar, Mohammed Garba ya bayyana cewa bashi da labarin wannan rikici bal ya samu labarin cewa yan kwankwasiyya sun shirya tayar da kura a wurin.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng