Dandalin Kannywood: Yadda harkar fim ta maida ni mutunniyar kirki - Jaruma Halima Ibrahim
Dama dai masu iya magana sun ce abincin wani, gubar wani. Yayin da jama'a da dama ke ikirarin cewa harkar fina-finan Hausa ba abunda suke jazawa al'ummar Hausawa sai lalacewar tarbiyya, daya daga cikin jaruman mai suna Halima Ibrahim ta ce kwata-kwata ba haka bane.
Jaruma Halima Ibrahim a cikin wata fira da tayi da majiyar mu ta bayyana cewa ita dai kam harkar fim ma gyara mata tarbiyya tayi ta kuma maida ta mutunniyar kirki.
Legit.ng ta samu dai cewa jarumar da ta bayyana cewa yanzu haka ta fito a fina-finai akalla 20 ta kuma ce harkar fim itace ta koya mata hakuri, zama da mutane, da kuma kai zuciya ne sa da a da bata da su.
Jaruma Halima Ibrahim ta ci gaba da cewa ita yanzu har iyayen ta ma dai mamakin kyawawan halayen ta suke yi tun bayan shigar ta harkar fim din gadan-gadan.
Tun farko dai jarumar ta bayyana cewa ta dade tana sha'awar harkar ta fina-finan tun tana karama amma bata fito ta fadawa iyayen ta ba sai da ta kammala karatun ta na Digiri a jami'a.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng