Manyan Malaman Najeriya sun yi wa Kasar addua a wajen aikin Hajji
- Malamai sun hada kai wajen yi wa Najeriya addua a Saudiyya
- Shugaban Izala da Malaman Tarika duk sun sa kasar a addua
- Wasu Gwamnonin kasar da Sanatoci su na cikin masu halarta
Mun ji cewa manyan Malaman Najeriya sun yi wa Kasar nan da Shugaba Buhari addua a wajen aikin Hajji dazu.
Labari ya zo mana daga shafin Kungiyar Izala cewa Malamai da dama sun yi wa kasar addua a karkashin jagorancin Shugaban Maniyyatan kasar na bana watau Sarkin Bauchi Mai Girma Rilwanu Sulaiman Adamu.
KU KARANTA: Gobe ake Sallah a Duniyar musulunci
Malaman da su ka halarci wannan addua sun hada da Sheikh Abdullahi Bala Lau da kuma Sheikh Tijjani Bala Kalarawi da Sheikh Dahiru Bauchi da sauran su. Wasu Gwamnonin kasar irin su Gwamnan Jigawa da Bauchi da Sanatocin Borno da Zamfara su na cikin taron.
Duk wani Mahajjaci a wannan rana yana dukafa ana kuma neman rahamar Allah. Ana son azumi ga wadanda ba su je Hajji ba wanda ke kankare zunuban shekara biyu.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Beraye sun kora Shugaba Buhari daga ofis
Asali: Legit.ng