Manyan ibada guda 7 da ake bukatar Musulmi yayi a ranar Arafa
Akwai wasu muhimman ibadoji guda 7 da ake bukatar dukkanin Musulmi yayi a ranar 9 ga watan Zulhijja, wato ranar Arafa, wanda aka fi sani da jajibarin Sallah.
Jaridar Premium Times Hausata ruwaito wadannan manyan ibadu da Musulmi ya kamata ace yana yi, kamar yadda Imam M Bello Mai- Iyali ya kawo su.
KU KARANTA: Yau take ranar Arfa: An canza ma Ka’abah riga (Hotuna/bidiyo)
Daga cikin muhimman ibadun nan akwai:
1- Tsayuwa a filin Arafa ga mahajjata
2- Azumin ranar Arafa ga mai zaman gida
3- Istigifari da neman tuba
4- Yin nesa daga aikata zunubai da sauran miyagun ayyuka
5- Yawaita ambaton Ubangiji ta hanyar zikiri
6- Kyautata ma jama’a, musamman marayu
7- Addu’a! Addu’a!! Addu’a!!!
Majiyar Legit.ng ta ruwaito wani hadisin Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a garshi yana cewa “Mafi alherin addu’a itace ta ranar Arafa…”
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng