An doke Bill Gates a matsayin wanda yafi kowa arziki a duniya
-Mr Amancio Ortega ne mutumin da yafi kowa kudi a duniya a yanzu
-Mr Ortega dai ya doke Bill Gates ne bayan hannun jarin kamfanin sa mai suna Inditex yayi tashin gauron zabi
-Mr Ortega ya kafa kamfaninsa na farko ne tareda martarsa Rosalia a shekarar 1975
A sabon rahoton da jaridar Forbes ta fitar ranar Laraba, mai kamfanin Zara, Amancio Ortega ya doke attajirin duniya Bill Gates wurin zama mutumin da yafi kowa arziki a duniya yanzu.
A yanzu Ortega ya 'dara Bill Gates kudi da dallan Amurka miliyan 200 a dalilin tashin gwauron zabi da hannun jarin wata kamfanin mai suna Inditex tayi a makon da ya wuce, Inditex ne ta raini kamfanin Zara mallakan Ortega.
Jaridar Forbes tace Mista Ortega ya zama mutumin da yafi kowa kudi a duniya sau uku a baya amma ana doke shi a cikin kwana daya.
DUBA WANNAN: Kishin-kishin: Dangote ne dan takarar a PDP 2019
Duk da razikin Mr Ortega, mutane da yawa basu san shi ba.
An dai ce shi mutum ne shiru-shiru kuma bai cika shiga cikin mutane ba, a duk tsawon rayursa hirar da yayi da yan jaridar tsiraru ne.
Mista Ortega ya fara sana'ar sa ne a shekarar 1975 a yayinda suka fara kamfanin kayan sawa tare da matan sa a wannan lokacin mai suna Rosalia.
Sauran rassan kamfanonin sa sun hada da Mussimo Dutti da Pull & Bear wanda ke da rassa guda 7,385 a fadin duniya.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng