Kungiyar NLC ta bukaci ayi kakkaba a majalisar Buhari

Kungiyar NLC ta bukaci ayi kakkaba a majalisar Buhari

- Shugaban kungiyar NLC, Kwamrad Ayuba Wabba, akwai bukatar ayi kakkaba a majalisar Buhari bayan shekaru biyu domin a cire ministoci da basa aiki

- Wabba ya bayyana cewa yawancin yan Najeriya sun sa ran cewa gwamnatin Buhari zata kara kaimi a gwamnati

Kungiyar kwadago na Najeriya (NLC) tayi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari day a kori wasu daga cikin ministocinsa wadanda basa aiki.

Shugaban kungiyar ta NLC, Kwamrad Ayuba Wabba, yayi wannan kira a wani rahoto da aka wallafa a jaridar Nigerian Tribune a ranar Talata, 28 ga watan Agusta, yayinda yake Magana kan tsanmanin kungiyar kwadagon daga gwamnatin Buhari.

Wabba yace akwai bukatar yin kakkaba a gwamnatin Buhari bayan shekaru biyu domin a tsige ministocin da basa aiki.

Kungiyar NLC ta bukaci ayi kakkaba a majalisar Buhari
Kungiyar NLC ta bukaci ayi kakkaba a majalisar Buhari

Da yake yima shugaban kasar murnar dawowa bayan hutun jinya na sama da kwanaki 100 a kasar waje, shugaban kungiyar kwadagon yace tashin hankali yayi yawa a lokacin da ake ta wakar dawowar Buhari saboda akwai tsamanni da dama daga yan Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Allah yayi ma tsohon Sanata Kanti Bello rasuwa

Wabba ya bayyana cewa akwai al’amura dake da alaka da rashawa da dama da ba’a kammala ba, ya kara da cewa akwai bukatar a kaddamar da yawan kudaden da aka samo.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng