Wani Dan baiwa ya kirkiro keke mai kama da babur a Najeriya

Wani Dan baiwa ya kirkiro keke mai kama da babur a Najeriya

- Wani Saurayi ya kirkiro keke mai kama da babur

- An ga wannan abun fasahar ne a can Jihar Borno

- Wannan zai taimaka kwarai wajen watayawa a Gari

A can Jihar Borno da ke Arewa maso gabashin Kasar nan wani Saurayi dan baiwa ya kera keke mai injin babur.

Wani Dan baiwa ya kirkiro keke mai kama da babur a Najeriya
An kirkiro keke mai gudu tamkar babur

Labarin wani mai fasahar tsiya ya kai gare mu daga Jaridar nan ta Rariya inda aka kera keke mai gudu kamar babur. Wannan keke na aiki ne da Inji na janareta wanda sai dai kurum ka murza ba tare da taka feda ba ana wahala abin cikin sauki.

KU KARANTA: Ka ji makiyan Buhari a Najeriya

An kera wannan keke ne a Garin Maiduguri da yake babban Birnin Jihar Borno. Ba shakka irin wannan keke zai taimakawa wajen yawatawa a musamman cikin Garin inda tuni aka hana ganin babur na yawo a dalilin rikicin Boko Haram.

Kwanaki a Warri wani Mutumi mai basirar jaraba ya maida Babur dinnan da ake kira Keke Napep mai kafafu uku jirgin saman helikwafta. Wannan mutumi dai da hannun sa yayi wannan aiki, hakan ta sa har aka kira Gwamnati ta dafa masa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Beraye sun hana shugaba Buhari shiga ofis?

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel