Sabon rikici ya barke a jam'iyyar APC ta jihar Taraba
Yanzu haka labaran da muke samu daga majiyoyin mu daban daban na nuni da cewa sabon rikici ya sake barkewa a jam’iyar adawa ta APC dake a jihar Taraba dai dai lokacin da tsohon mukaddashin gwamnan jihar Garba Umar ya koma jam’iyar.
Barkewar rikicin kuma ke da wuya sai wasu daga cikin kusoshin jam’iyar ta APC a jihar suka balle suka kuma kafa wata sabuwar abun da suka kira 'tafiya' da kuma suka kira kansu kungiyar yan 'integrity' watau gaskiya da rikon amana.
Legit.ng dai ta samu cewa su dai wadanda suka balle din sun hada da tsoffin Sanatoci da tsohon shugaban jam’iyar a jihar da yan wasu Majalisu da kuma masu ruwa da tsaki a siyasar jihar da dama inda kuma suka ce sun kafa wannan sabuwar tafiyar ne domin su ceto jam’iyar daga halin ha’ulai da suka ce wasu sun jefa ta a ciki.
To sai dai kuma a wani kakkausan martanin da dayan bangaren na jam'iyar ya maida, wanda ke zaman shugaban riko na jam’iyar a jihar, Alhaji Sani Chul da dama can yana tare da ministar harkokin mata da walwalar jama’a Aisha Jummai Alhassan, ya musanta zargin cewa basa tafiya da kowa.
Asali: Legit.ng