Dandalin Kannywood: Da ba don fim ba da yanzu na zama farfesa - Jarumi Bosho

Dandalin Kannywood: Da ba don fim ba da yanzu na zama farfesa - Jarumi Bosho

Shahararren jarumin nan dan wasan barkwanci na fina finan Hausa a masana'antar Kannywwod watau Sulaiman Yahaya wanda aka fi sani da Sule Bosho ya fito fili ya shaidawa duniya cewar shigar da ya yi a cikin harkar fim ce musabbabin hana shi zama farfesa kawo yanzu.

Da yake bayar da ba'asi game da musabbabin inda ya samo sunan sa na Bosho, say jarumin ya kada baki yace: "Na samo sunan Bosho ne saboda sadda nike makarantar gaba da firamare watau sakandare ina yawan yin karatu. Wani lokaci ma har nikan kwashe kusan kwana 40 ban yi cikakken bacci ba."

Dandalin Kannywood: Da ba don fim ba da yanzu na zama farfesa - Jarumi Bosho
Dandalin Kannywood: Da ba don fim ba da yanzu na zama farfesa - Jarumi Bosho

Legit.ng ta samu cewa jarumin ya shaidawa majiyar mu cewa shigar sa harkar fina-finan Hausa ce ta hana shi zama farfesa kawo yanzu.

Haka ma dai jarumin ya bayyana cewa sha'awarsa wajen karatu ce ta sanya yake amfani da kalmomin 'yan boko a fina-finansa.

Daga karshe kuma jarumin ya bayyana ainihin alakarsa da marigayi Alhaji Rabilu Musa Ibro inda ya bayyana cewa akwai dangantaka mai kyau tsakaninsu. Kafin ya rasu mu kan bai wa juna shawara kan al'amuran rayuwa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng