Naman gwangwani da madara berayen Aso Rock ke ci – Shehu Sani yayi ma fadar shugaban kasa ba’a
- Sanarwar cewa shugaba Buhari zai dunga aiki daga gida sakamakon gyare-gayre da za’ayi na ci gaba da janyo cece-kuce
- Sanata Shehu Sani ya soki bayanin da fadar shugaban kasa tayi cewa hakan cin zarafi ne
- Sanatan ya wallafa wani rubutu a shafin Facebook, inda yayi ba’a kan al’amarin
Sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya yi ba’a ga rahotannin dake cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai iya aiki a ofishin sa ba saboda baraye da sukayi barna.
Da yake maida martani kan al’amarin, sanatan yayi ba’a cewa barayen fadar shugaban basa bazasu kasance irin wadanda ake gani a Nyanya, wani yanki mai cinkoson jama’a a Abuja.
A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook, dan majalisar yace barayen fadar shugaban kasa naman gwangwani da madara suke sha.
KU KARANTA KUMA: Ra'ayoyin yan Najeriya game da berayen da suka hana shugaba Buhari shiga ofishin sa
A baya kakakin shugaban kasa, Garba Shehu ya bayyana cewa shugaban kasa zai dunga aiki daga gida saboda ana gyare-gyare a ofishin sa sakamakon barna da beraye da kwari suka yi.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng