Zalunci ko Hauka? Wani mutum ya kashe dan da suka haifa domin ya hukunta matar

Zalunci ko Hauka? Wani mutum ya kashe dan da suka haifa domin ya hukunta matar

-Wani mutum a kasar Amurka yayi wa dansa kisar gila domin ya bakantawa uwar dan rai

-Kotu ta yanke masa shekaru 25 a gidan kurkuku

-Matar tasa ta tsine masa Albarka kuma tayi masa fatan dawama a wuta

Kotu ta yanke wa wani mutum dan asalin California, mai suna Aramad Andressian zaman shekaru 25 a gidan kaso saboda kashe dan sa mai shekaru 5 domin kawai ya bata wa Uwar yaron rai.

Masu bincike sunce Andressian ya amsa laifin kisan dan nasa wanda hakan yasa matar tasa tayi ta tsine masa albarka a lokacin da kotun yankin Los Angeles take sauraran karar.

Wani mutum ya kashe dan sa domin ya musguna wa matar sa
Wani mutum ya kashe dan sa domin ya musguna wa matar sa

"Fata na shine kayi ta ganin fuskan da na da ka kashe a kowane rana har karshen rayurka mara amfani, Koma ina fata ruhin ka ya dawamma a cikin wuta" Inji Uwar dan Ana Estevez.

Matar har ila yau, tace mijin nata ba uba nagari bane kuma bashi da wani amfani ma ga alumma.

"Bana jin wani ciwo a tare dani, kawai dai rayuwar duk bata min dadi, ji nakeyi kamar mutuwa nayi yadda da na ya mutu," inji ta

DUBA WANNAN: Yan Najeriya milyan 57 suna fama da rashin ruwan sha mai tsafta - UNICEF

Andressian, mai shekaru 35 a duniya ya amsa laifin kisan gila da yayi wa dan sa a watan Aprilu bayan sun dawo daga wani wurin shakatawa da ake kira Disneyland.

Andressian ya amsa laifin sa saboda yana tsoron kotu ta yanke masa hukunci kisa shima, a cewar lauyansa. Uban dai bai ce komai ba a lokacin da alkalin kotun Alhambra yake yanke masa hukunci, kamar yadda kamfanin dilancin labaran Fox 11 ta bada rahoto.

Masu bincike sun kwashe watanni biyu suna neman dan kafin daga bisani suka tsinci gawar tashi a kusa da wani kududufi da ke kusa da Santa Barbara.

Lauyoyi masu shigar da kara basu fada yadda yaron ya mutu ba amma alamu sun nuna cewa da gangar aka kashe yaron, sai dai lauyan Andressian, Ambrosio Rodriguez ya sha nanatawa cewa cewa ba da gangar uban ya kashe dan ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel