Magani 5 da tafarnuwa ke yi a jikin dan Adam
Binciken masana kiwon lafiya da masana abinci sun bayyana irin nau'ikan magani da tafarnuwa ke bayarwa ga jikin dan Adam
Tafarnuwa ba ta tsaya wajen karin dandano ga abinci kadai ba, domin ta na da adadi na fa'idoji na magani a jikin dan Adam. A yau shafin Legit.ng ya kawo muka muhimman amfani na magani da tafarnuwa ke yi a jikin dan Adam.
1. Tafarnuwa na maganin Ciwon Zuciya
An gano cewar tafarnuwa na zama mai bayar da kariya da kuma kulawa ga cututtukan zuciya, ciki har da atherosclerosis, hyperglycemia, thrombosis, hauhawar jini da ka iya janyo bugun zuciya.
2. Tafarnuwa don Ciwon daji
Yawancin nazari ya nuna alaka tsakanin karuwar amfani da tafarnuwa wajen rage hadarin ciwon daji na ciki, ciwon kogi, karamin hanji da babba, da kuma cutar daji ta mama.
3. Tafarnuwa don ciwon hawan jini mai tsanani
Bincike akan tafarnuwa ya nuna irin taimakon da ta ke bayarwa wajen kawar da cutar hawan jini. Daya daga cikin binciken ya nuna cewar amfani da rikakkiyar tafarnuwa a kullum har na tsawon watanni uku yana sanyan hawan jini ya sauka a jikin mutum.
KU KARANTA: Masu garkuwa da mutane sun nemi Naira Miliyan 100 kudin fansar wata 'yar shekara 11
4. Tafarnuwa don sanyi da cututtuka
Tafarnuwa tana da matukar tasiri wajen kashe wasu kananan kwayoyin halitta da ke da alhakin dorawa mutum ciwon sanyi. Tafarnuwa a zahiri tana taimakawa wajen hana sanyi da sauran cututtuka. Akwai sunadarai na antimicrobial da antiviral da suke kunshe a cikin tafarnuwa wadanda su ne suke taimakawa wajen kawar da sanyi da sauran cututtuka masu alaka da sanyi.
5. Tafarnuwa ga Ciwon sukari
Cin danyar tafarnuwa yana taimakawa wajen daidaita tsarin sukari na cikin jini, wanda zai iya dakatarwa ko rage yawan tasirin wasu matsalolin ciwon sukari, da kuma yaki da cututtukan wadanda daskararren maiko ke janyowa (cholesterol) da karfafa zagayen jini a tashoshin sa.
Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng