Na shiga harkar fim ne domin wa'azi da fadakarwa - Inji sabuwar jaruma Amina Yola

Na shiga harkar fim ne domin wa'azi da fadakarwa - Inji sabuwar jaruma Amina Yola

Wata sabuwar fuska da ta bulla a masana'antar Kannywood na fina-finan Hausa mai suna Amina Yola ta bayyana sha'awar yin wa'azi da kuma fadakarwa ga al'umma a matsayin muhimman dalilan da suka sa ta tsunduma a harkar fim gadan-gadan.

Jarumar ta bayyana cewa ta dade tana muradin ganin yadda zata iya bayar da tata gudummuwa ga cigaban al'umma musamman yadda ta ke ganin yan fim din na yi tun tana yarinya.

Na shiga harkar fim ne domin wa'azi da fadakarwa - Inji sabuwar jaruma Amina Yola
Na shiga harkar fim ne domin wa'azi da fadakarwa - Inji sabuwar jaruma Amina Yola

Legit.ng ta samu kuma cewa matashiyar sabuwar fuskar ta bayyana cewa bata shiga harkar fim ba sai da ta samu izinin yin hakan daga wajen iyayenta, inda kuma ta kara da cewa harkar fim din harka ce da ke da bukatar hakuri musamman ganin cewar ana mu’amala da mutane da dama.

Haka ma dai jarumar ta bayyana shararriyar jaruma Hadiza Gabon a matsayin wadda take so ta kwaikwaya sannan kuma tace yanzu haka abun da ta sa a gaba kenan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel