Kasar Saudiyya na bukatar dabbobi 120,000 duk sati daga Najeriya
- Kasar Saudiyya na bukatar dabbobi 120,000 duk sati daga Najeriya
- Gwamnan banki ya bayyana yadda za a kulla harkallar kasuwanci da wasu kasashen waje
- Ga duk mahajjati wajibi ne ya yanka dabba a kasar Saudiyya yayin aikin hajji
Gwamnan babban bankin kasa, Godwin Emefiele, ya bayyana hakan a yayin da yake gabatar da lakca a kan kalubalen masassar tattalin arziki da ribar da za a iya girba daga hakan, yayin da ya halarci taron lauyoyi na kasa a Legas.
Emefiele, ya bayyana cewar yanzu haka akwai yawaitar kasashe da ke kokarin kulla harkallar kasuwanci da Najeriya.
Emefiele, yace 'a misali, akwai bukatar naman halal daga kasashen larabawa da dama. A takaice muna da sahihin bayani cewar kasar Saudiyya zata bukaci kan dabbobi 120,000 duk sati.'
DUBA WANNAN: Duba Tsabar Kudin Da Gwamnatin Saudiyya Ta Biya ga Alhazan Da Aka Ciwa Mutunci
Kasar Saudiyya ce a farko cikin jerin kasashen duniya da ke sayen dabbobi daga kasashen ketare. Kasashen Sudan da Somalia ne ke samar wa Saudiyya mafi yawan dabbobin da take bukata. A shekarar 2016 kasar ta Saudiyya ta bawa kasar Zambiya kwangilar samar da awakai miliyan 1 duk wata.
A duk shekara miliyoyin jama'a ke halartar aikin hajji a kasar Saudiyya, kuma wajibi ne ga duk mai aikin hajji ya sayi tare da yanka dabba a kasar.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng