Ma'aikatan banki sama da 300 ake kora daga aiki kowane mako a Najeriya

Ma'aikatan banki sama da 300 ake kora daga aiki kowane mako a Najeriya

- Masu aiki a banki na fuskantar mugun hadari a Najeriya

- Ma'aikatan banki da dama ake fatattaka daga aiki a Najeriya

- Hukumar NBS ta Kasar ce tayi wannan nazari a shekarar bana

Wani nazari da Hukumar NBS tayi ya nuna cewa Ma'aikatan banki su na cikin dar-dar a Kasar nan.

Ma'aikatan banki sama da 300 ake kora daga aiki kowane mako a Najeriya
Masu aiki a bankuna su na cikin wani hali mai ban tsoro

Masu aiki a bankuna su na cikin wani hali mai ban tsoro a Najeriya don kuwa a ko yaushe ana iya korar su daga aiki. Hukumar tace Ma'aikatan banki 340 ake fatattaka daga aiki a kowane mako a fadin Najeriya. Ana dai fama da rashin aikin yi a Najeriya.

KU KARANTA: An dade babu albashi a Adamawa

Daga farkon shekarar nan zuwa yanzu an kori ma'aikatan banki 8,663 a fadin kasar. Mafi yawan wadanda ake sallama daga aikin kananan Ma'aikata ne kamar yadda nazarin ya nuna. Hukumar NBS ta Kasar ce tayi wannan nazari. NBS ta fitar da wannan rahoto ne a farkon makon nan.

Kun ji cewa Farfesa Yemi Osinbajo ya nemi 'Yan Najeriya su rika biyan haraji ko kuma su gamu da fushin Hukuma. Mataimakin Shugaban kasar ya bada wa'adin wata uku ga wadanda ba su biyan haraji da su tuba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Farashin kaya ya tsawwala a Najeriya

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng