Kalli Hajara Bashari, Bahaushiya musulma ta farko da ta kai matakin kwamanda a Najeriya (hotuna)

Kalli Hajara Bashari, Bahaushiya musulma ta farko da ta kai matakin kwamanda a Najeriya (hotuna)

Hajara ta fara aiki a matsayin jami’ar soja a 1986. Ta samu daukaka inda ta kasance bahaushiya kuma musulma ta farko daga yankin arewa da ta fara kai wa matsayin kwamanda, wanda yayi daidai da matsayin kanal a soja.

Hajara, yar marigayi Marafan Birnin Kudu, Kanall Bashari Umaru daga Birnin Kudu a jihar Jigawa, yanzu ita ce shugaban ma’áikatan jinya na asibitin sojoji dake Kano. Ta taba zuwa yaki a Congo, daga cikin wuraren da tayi aiki akwai Ibadan da Kaduna.

An haife ta ne a Dorayi Quarters a ranar 19 ga watan Maris, 1964, ta girma ne a Yakasai Quarters a Kano, sannan ta fara karatun firamare a Wagwarwa Primary School, sannan ta koma St. Louis Primary School.

Kasancewarta daliba mai ilimi, Hajara ta samu shiga Queen’s College, Lagos da St. Louis Secondary School, Kano. Ta zabi karatu a Kano ne saboda sauyin aikin da mahaifinta ya samu zuwa Kano. Bayan ta kammala da karatun sakandare ne ta shiga makarantan koyon jinya a Kano.

Kalli Hajara Bashari, Bahaushiya musulma ta farko da ta kai matakin kwamanda a Najeriya (hotuna)
Kalli Hajara Bashari, Bahaushiya musulma ta farko da ta kai matakin kwamanda a Najeriya

A cikin makarantan ne ta yanke shawarar shiga aikin sojojin sama wanda ya biyo bayan neman kwasan ma’aikatan kula da lafiya.

KU KARANTA KUMA: Yan bautar kasa sun ziyarci makarantar firamare a Kano inda dalinbai ke karatu a kasa (hotuna)

‘’Babu shakka hakan ya kasance abun al’ájabi. Mahaifiyata bata so hakan ba ko kadan. Mahaifina ya amince ne kawai domin faranta mun rai. Amman ya karfafa mun gwiwa, ya kuma girmama zabin da nayi." Inji ta.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng