Yan bautar kasa sun ziyarci makarantar firamare a Kano inda dalinbai ke karatu a kasa (hotuna)
Wani dan bautar kasa Precious Igbinedion wanda ke bautar kasar sa a wani makarantar firamare dake Dambatta, jihar Kano ya buga hotunan makarantar da aka tura shi.
Daliban na zama ne a kasa a yayinda ake koyar dasu karatu. Wannan ya nuna yanayin tsarin iliminmu da kuma yadda makarantun da ake karantar da yara yakan kasance.
A cikin kokari da yan bautar kasa keyi na tallafa wa al’umma musamman a karkara, sun rarraba ma yaran takardun rubutu da kayayyakin karatu.
KU KARANTA KUMA: Tunatarwa: Ranar Alhamis za’a yi tsayuwar Arfa a Saudiyya
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng