Tunatarwa: Ranar Alhamis za’a yi tsayuwar Arfa a Saudiyya

Tunatarwa: Ranar Alhamis za’a yi tsayuwar Arfa a Saudiyya

- Saudiyya ta ba da sanarwa a kan ranar Arfa

- Ranar Alhamis 31 ga watan Agusta za'ayi tsayuwar Arfa

- 1 ga watan Satumba zai kama ranar sallar Layyah

Rahotanni sun kawo cewa gwamnatin kasar Saudiyya ta yi magana a kan ranar da za’ayi tsayuwar Arfa, inda ta bayyana cewa ba’a ga jinjirin watan Dhul-Hijjah a kasar a ranar Litinin ba kamar yadda akayi zaton sa a lissafin kalandar kasar.

A cewar shafin Alummata, wannan dalili ne yasa yau Talata zai zamo 30 ga watan Zul-qaada, wato kenan ranar Arafah zai kama ranar Alhamis 31 ga watan Agusta, sannan ranar Juma’a, 1 ga watan Satumba zata zama ranar Sallar layya a kasar.

Tunatarwa: Ranar Alhamis za’a yi tsayuwar Arfa a Saudiyya
Tunatarwa: Ranar Alhamis za’a yi tsayuwar Arfa a Saudiyya

KU KARANTA KUMA: Don murnar dawowar Buhari, wadannan yan Najeriyan sunyi liyafa da naman akuya (hotuna)

Har ila yau a kasar Najeriya, ranar Yau Talata, shine 29 ga watan Dhul-qaada a lissafin ganin wata, sannan kuma a yau ne sarkin musulmi, Alhaji Muhammad Abubakar Sa’ad ya bada sanarwar a fara neman jinjirin wata a fadin kasar baki daya.

Da fatan idan an gani za’a sanar da mahukunta har ya kai ga sarkin na musulmai.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel