Wani Boka ya bayyana abin da ya sa Ronaldo ke samun matsala

Wani Boka ya bayyana abin da ya sa Ronaldo ke samun matsala

- Wani Boka ya bayyana abin da ya ja wa Cristiano Ronaldo tasgaro

- Yace Dan wasan bai bar alaka mai kyau tsakanin sa da uban sa ba

- Mahaifin na sa ya rasu ne lokacin yana bugawa Manchester United

NAIJ Hausa na da labari cewa wani Boka ya bayyana abin da ya sa Ronaldo ke samun matsala a rayuwar sa.

Wani Boka ya bayyana abin da ya sa Ronaldo ke samun matsala
Babban Dan wasa Cristiano Ronaldo

Fernando Noguiera wani kasurgumin Boka da aka fi sani da suna Fafe yace tsinuwar Mahaifin Cristiano Ronaldo ce ta ke bin sa. Ronaldo dai bai halarci jana'izar Mahaifin sa ba a lokacin yana bugawa Kungiyar Manchester United kalo yana dan shekara 20 a Duniya.

KU KARANTA: Ronaldo zai gamu da fushin hukuma

Wani Boka ya bayyana abin da ya sa Ronaldo ke samun matsala
Dan wasa Ronaldo a wani wasa

Bokan yace alakar Dan wasan da Mahaifin sa ne ya jawo masa halin da yake ciki a yanzu. Ronaldo dai ya samu matsala da Mahaifin sa wanda shan giya yayi sanadiyar mutuwan sa. Fafe yace dole Ronaldo ya nemi wani Boka da zai gyara karin ko kuma yayi ta samun matsala.

Kwanaki aka shiga Kotu da babban Dan wasan Real Madrid Cristaino Ronaldo inda ake zargin sa da laifin rashin biyan haraji a Kasar Sifen.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ana murnar dawowar Shugaban kasar Najeriya

Asali: Legit.ng

Online view pixel