Allah ya yi wa dan Salihu Sagir Takai rasuwa
Allah ya yi wa wani dan bautar kasa, Ibrahim Salihu Sagir Takai rasuwa a yammacin jiya Lahadi, 20 ga watan Agusta a jihar Kano.
Baá sanar da abunda ya haddasa mutuwar tasa ba amma an sanar da mutuwarsa ta shafin Facebbok.
Za’a yi jana'izar sa a yau Litinin, 21 ga watan Agusta a gidan Malam Salihu Sagir Takai dake Hadejia Road (daura da Buhari Shoping Complex Kano.
Allah ya gafarta masa Allah ya sa aljanna makoma.
![Allah ya yi ma dan Salihu Sagir Takai rasuwa Allah ya yi ma dan Salihu Sagir Takai rasuwa](https://cdn.legit.ng/images/1120/vllkyt101k88du6jf8.jpeg?v=1)
Abokansa sun nuna alhini da jimami na wannan babban rashi da sukayi.
KU KARANTA KUMA: Wani mutumi ya zuba Mirinda a kasa ya sha don murnar dawowar Buhari (hoto)
Daya daga cikin abokansa mai suna Abba Mansur ya buga hotonsa tare da marigayin a shafinsa na Faceboo hade da sakon ta'aziyya.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng