Rikici na nema ya barke tsakanin magoya bayan Barcelona

Rikici na nema ya barke tsakanin magoya bayan Barcelona

- A halin yanzu Kungiyar Barcelona na shirin shiga rikici

- Magoya bayan Kungiyar na nuna cewa ba su ji dadi

- Kwanan nan kuma dai Real Madrid ta lallasa Barcelona

Magoya bayan Kungiyar Barcelona na nuna cewa ba su ji dadin abin da ke faruwa a kulob din. Kuma har yau dai Dan wasa Lionel Messi ba kara kwantiragi da Kungiyar ba.

Rikici na nema ya barke tsakanin magoya bayan Barcelona
Shugaban Kungiyar Barcelona

Idan dai ba ayi wasa ba dai kamar yadda mu ka fahimta za a samu matsala da Kungiyar Barcelona inda wasu magoya bayan ke nuna rashin jituwa ga abubuwan da ke faruwa a Kulob din. Wannan na zuwa ne bayan abokan gaba Real Madrid ta lallasa Kungiyar.

KU KARANTA: Me ke sa Nafisa shaye-shaye

Rikici na nema ya barke tsakanin magoya bayan Barcelona
Barca tayi asarar Dan wasan ta Neymar

Kungiya tayi asarar Dan wasan ta Neymar Jr. Haka kuma Kungiyar ta buge da sayen Dan wasa Paulinho na kasar Brazil. Wasu dai ba su ji dadin wannan sayayya ba su kace akwai wata makarkashiya kuma wasu sun kira dama a tsige Shugaban Kungiyar.

A shekaran jiya dai Kungiyar Real Madrid ta doke Barcelona gida da waje a kofin Super Cup na kasar a gasar shekarar bana ta dauki kofi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ana bukatar Jami'ai a coci?

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Tags: