Ruwan roba yana haifar da cututtukan hakori

Ruwan roba yana haifar da cututtukan hakori

Wata sabuwa kuma, domin bincike ya nuna cewa shan ruwan roba yana haifar da matsalar cutar hakori

Kamar dai yadda aka sani, kayan zaki ba su barin hakori ya zauna lafiya kuma ruwa musamman ma na roba ana alakanta shi da mafi tsafta a cikin ruwan sha na mutane, sai dai ba anan fagen dagar ya ke ba.

Likitocin hakori sun bayyana cewa amfani da ruwan roba yana haifar da lalacewar hakori.

Bincike ya nuna cewa, da yawa daga cikin ruwan roba suna da karancin sunadarin Fluoride wanda rashin na sa yana gurbata hakori.

Ruwan roba yana haifar da cututtukan hakori
Ruwan roba yana haifar da cututtukan hakori

Sakamakon bincike da aka gabatar a jami'ar Martin Luther, da cibiyar bincike (Biotechnology Research and Information Network AG, BRAIN AG) ne su ka bayyana hakan a wata mujalla ta bincike akan hakori.

Wani likitan hakori kuma, Dr. Eunjung Jo, ya bayar da rahoto a wata mujalla ta DAILY MAIL ya gargadi shan ruwan mai kunshe da guba yana gurbata hakori.

KU KARANTA: 'Yan sanda sun cafke wani mutum da kan wata mace a jihar Legas

Ya ce, ruwan gwamnati da yake kwarara ta famfo, yana kunshe da sunadarin Flouride, wanda shi kuwa ruwan roba ya rasa, kuma rashin wannan sunadari a cikin ruwa shi ke maishe da ruwa ya zamto mai kunshe da guba.

Cibiyar kula da yaduwar cututtuka (Center for disease Control, CDC) ta kasar Amurka ta bayyana cewa, yara da suke rayuwa a yankunan da ruwan famfon su ba shi da sunadarin flouride yana gadar mu su a rubewar hakori.

Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng