Anyi artabu tsakanin Sojoji da askarawan Biyafara a Anambra (Hotuna)

Anyi artabu tsakanin Sojoji da askarawan Biyafara a Anambra (Hotuna)

- Dakarun Sojin Biyafaraa sun gwada kwanji da jami’an tsaron Najeriya a Anambra

- Ana rade radin cewa an jikkata da dama daga cikinsu, tare kashe mutum daya

Rahotanni sun bayyana cewa an samu gawar mutum daya bayan wani arangama da aka yi tsakanin Sojojin Najeriya da Yansandan Najeriya a hannu guda, da kuma yayan kungiyar IPOB dake karajin kafa kasar Biyafara.

Wannan karanbatta ya wakana ne a garin Ekwulobia dake karamar hukumar Aguata na jihar Anambra yayin da yan IPOB ke dakon zuwan shugabansu, Nnamdi Kanu garin don wayar musu da kai akan kada su bari ayi zabe a garin.

KU KARANTA: Kimiyya da fasaha: An ƙera wata motar ‘Tasi’ mai a sararin samaniya

Legit.ng ta ruwaito shugaban IPOB na fadin ba zasu taba bari a yi zabe a Anambra ba wanda ake sa ran yi a ranar 18 ga watan Nuwamba, idan dai ba’a fara yin zabe raba gardama ba don samar da kasar Biyafara.

Anyi artabu tsakanin Sojoji da askarawan Biyafara a Anambra (Hotuna)
Sojoji da askarawan Biyafara

Tun da misalin karfe 8 na safe ne jami’an tsaro suka dira garin Ekwulobia cikin motoci 14m sai dai hakan bai hana yan IPOB hidindimunsu ba, suna wake waken yaki tare da daga tutar Biyafara. Daga nan ne sai yan IPOB suka nemi su kai ma jami’an tsaro, suka kuma bade su da barkonon tsohuwa.

Anyi artabu tsakanin Sojoji da askarawan Biyafara a Anambra (Hotuna)
Askarawan Biyafara

Kaakakin rundunar yansandan jihar Nkeiruka Nwode ta musanta jita jitan kashe wani a yayin rikicin, inda tace sun samu korafe korafe daga al’ummar yankin cewa wasu mutane sun rufe musu hanya, don haka aka aika da jami’a tsaro suka fatattake su, kuma suka bude hanyar.

Anyi artabu tsakanin Sojoji da askarawan Biyafara a Anambra (Hotuna)
Askarawan Biyafara

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ba za'a raba Najeriya ba, inji Osinbajo, Kalla:

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng