Hatsarin da cututtukan dabbobi ke jefa lafiyar mutane
Sanadiyar rashin ilimi na zamani, da yawa daga cikin al’umma masu kiwon dabbobi, ba su da masaniyar yadda rashin tsaftace muhallai da kuma rashin kula da lafiyar dabbobin su ke jefa lafiyar al’umma cikin hadurra.
Da yawa daga cikin mutane su na alakanta afkuwar cututtukan dabbobi da jadawali na rayuwa a madadin alakanta shi da rashin tsaftace wuraren kiwon na dabbobi wanda shi ne babban abinda ke haifar da cuta akan dabbobin.
Wani Farfesa Tunde Awoniyi, ya bayyanawa al’umma hakan a wani taron da aka gudanar a dakin taro na jami’ar fasaha ta Akure a jihar Ondo.
Awoniyi wanda masanin kiwon lafiyar al’umma ne da kuma tsaftar gonaki na kiwon dabbobi, ya ce, akwai alaka dake tsakanin lafiyar dabbobi da kuma lafiyar mutane domin akwai cututtukan abinci da sha da kwayoyin cuta na bacteria, virus da parasites suke shiga cikin jikin dabbobi da muke amfanuwa da naman su kuma su gadar mana da hatsari game da lafiyar mu.
Ya ce, sanadiyar wannan alaka dake tsakanin mutane da dabbobi, ya kamata al’umma su lura da tsaftar dabbobin da su ke kiwo don hakan zai taimaka wajen rage yaduwa ko kuma ballewar cuta ta hanyar gurbataccen nama na dabbobi marasa lafiya.
KU KARANTA: Bugun zuciya ya kama mijin wata mata sanadiyar keta ma sa haddi
Ya kara da cewa, ya kamata a lura da tsaftar dabbobi kama daga harkar kiwon su tun su na raye zuwa sarrafa naman su a wuraren saye ko amfani.
A karshe, Awoniyi ya yi kira ga gwamnatin tarayya a kan samar da ingatattun mayanka da kwata na zamani a kasar nan kamar irin na jihar ta su ta Ondo.
Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng