Kungiyar Real Madrid ta doke Barcelona gida da waje ta dauki kofi
- Kungiyar Real Madrid ta doke Barcelona gida da waje
- Real Madrid ta dauki kofin Super Cup na kasar jiya
- Barcelona ta sha kashi da jimillar ci 5-1 a kofin
A jiya dai Kungiyar Real Madrid ta doke Barcelona gida da waje a kofin Super Cup na kasar a gasar shekarar bana.
Real Madrid ta dauki kofin Super Cup na kasar a daren jiya bayan ta lallasa Barcelona a gida da waje. Barcelona ta sha kashi da jimillar ci 5-1 a kofin. A karon farko an doke Barcelona 3-1 sannan kuma a jiya aka tashi da ci 2-0.
KU KARANTA: Dan Najeriya zai tafi Landan a keke
Dan wasa Marco Asensio ne ya kara jefa kwallo wannan karo ana take wasan. Haka kuma Dan wasa Karim Benzema ya ci ta biyu. Irin su manyan 'Yan wasa Cristiano Ronaldo da Gareth Bale dai ba su buga wasan ba.
Jiya kun ji cewa Real Madrid za ta buga babu gwarzon Dan wasan ta Ronaldo bayan ya sha jan kati a wasan da aka buga Ranar Lahadi wanda har ya tura Alkalin wasa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Bikin Shekaru 20 da rashin Fela
Asali: Legit.ng