Fina-finan Kannywood da ya kamata ku kalla a wannan watan

Fina-finan Kannywood da ya kamata ku kalla a wannan watan

Watan Agusta ya zo da ruwan fina finai masu kayatarwa, daga masana'antar shirya finan finan hausa da a ke kira "Kannywood", da masu kallo ya kamata su nema don nishadin su.

1. Mata ta ce Shaida

Labari ne na wani magidanci da ke fuskantar tuhuma a gaban bisa zargin aikata laifin kisan kai, magidancin ya kasance bashi da wata shaida da zai gabatar domin gamsar da kotu a kan ba shi ya aikata laifin ba sai matar sa, hujja da a yawan lokuta kotu bata karba. Shin ko kotu za ta yi amfani da matar sa a matsayin shaida domin wanke shi daga zargin aikata laifin kisan kai?

2. Karamci

Shiri ne da yake nuna halayyar wasu iyaye wajen yi wa 'ya'yan su zabin abokin zaman aure.

3. Yar' Duniya:

Labarin wata tsintacciyar yarinya ce da wasu ma'aurata suka dauko daga gidan raino saboda basu samu haihuwa ba. Yarinyar ta taso cikin wadata da jin dadi, saidai bayan girmanta halayenta sun munana, sun saba da irin tarbiyyar da iyayen rikon nata suka bata.

Fina-Finai da na Kannywood da ya kamata ku kalla a wannan watan
Fina-Finai da na Kannywood da ya kamata ku kalla a wannan watan

4. Mijin yarinya:

Shirin yana nuni kan halin kunci da takura da 'yan mata masu karancin shekaru ke fuskanta wurin manyan 'ya'yan kishiyoyi yayin da aure ya kai su gidan yawa.

KU DUBA: Wani Mutum Ya Shirya Zuwa Ganin Buhari A Keke

5. Mansoor:

Shirin Ali Nuhu da tuni a ka nuna shi a manyan sanimomi tun karamar sallah. Labari ne da yake nuna halin tsangwama da kyama da yaran da a ka haifa babu aure ke fuskanta a rayuwa duk da kasancewar ba su suka zabi zuwa duniya ta wannan hanya ba.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a email dinmu na labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel