Mata biyu mafrauta sun dauki alkawarin kawo karshen ta’adanci a Taraba

Mata biyu mafrauta sun dauki alkawarin kawo karshen ta’adanci a Taraba

- Aisha tare da Halima suna neman amincewar gwamnati

- Mafarautan suna fuskantar matsalolin rashin makamai da motocin aiki

- Boko-haram na amfani da mugayen makaman zamani

Aisha Bakari da Habiba Husseini, yan mata biyu mafarauta sun ma gwamnatin tarayya alkawarin kawo karshen ta’adanci da masu garkuwa da mutane.

Yan matan sun bukaci gwamnati da ta tattauna da su dan basu dama.

Aisha da Habiba sun tabbatar da za su iya kawo karshen ta’adanci Boko-Haram a jihar Taraba.

Mata biyu mafrauta sun dauki alkawarin kawo karshen ta’adanci a Tarabai
Mata biyu mafrauta sun dauki alkawarin kawo karshen ta’adanci a Tarabai

A lokacin da mafarautan suka zanta da yan jaridan Vanguard, sunce "yaki da masu garkuwa da mutane da yan ta’ada yana bukatan makamai da kuma mutanen da suka san kan garin."

KU KARANTA: Me zai faru inda ace mutanen Buhari sun kashe Charley Boy-Fani Kayode

Aisha, wanda take kiran kanta da sunan sarauniyar mafarautan Adamawa ta ce ta na da abokan aiki dake kauyukan jihar, wanda suke ashirye dan hada kai da ita saboda yakan yan ta’ada.

“Abun da muke bukata, shine gwamnatin jihar ta zauna da kungiyan mu dan tattauna yadda za’a yi."

Ta ba da labarin yadda ita da mutanen ta, suka samu nasarar murkushe yan kungiyan Boko Haram a Arewacin Adamawa.

“Mutanen mu ashirye suke dan fafatawa da ‘yan ta’adan dake Madagali. Amma muna fuskantan karanci makamai da motocin aiki.

“Boko Haram suna amfani da mugayen makamai na zamani, amma mutanen mu basu da makaman da za su iya tunkarar su."

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: